An gano gawarwakin aƙalla mutane 61 bayan wani mummunan harin ‘yan bindiga da ya auku a ƙauyukan Bagna da Erena da ke ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja ta Nigeria.
Rahotanni sun nuna cewa mazauna yankin ne suka tattaro gawarwakin daga dazukan da ke kewaye da su, kwanaki bayan harin da ya haɗa da kashe mutane da kuma sace wasu. Daga cikin waɗanda suka mutu akwai jami’an tsaro, ‘yan bijilante da kuma farar hula. An riga an binne gawarwakin farar hula a Erena, yayin da na jami’an tsaro ke ajiye a ɗakin ajiyar gawa na Babban Asibitin Gwamnati da ke Minna.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa waɗanda abin ya shafa sun haɗa da jami’an tsaro da kuma mazauna gari, sai dai rundunar ‘yan sanda ta ce kisan ‘yansintiri uku ne kawai aka tabbatar.
Duk da haka, mazauna yankin sun yaba da kokarin jami’an tsaro da suka kawo ɗauki, amma sun soki gwamnati kan rashin ɗaukar matakin da ya dace duk da cewa an samu bayanan sirri kafin harin.
Harin ya kuma janyo ɗaruruwan mutane sun rasa matsugunansu, inda suka tsere zuwa makarantar Zumba Central Primary School da sauran wurare domin neman mafaka a yankin Shiroro.