Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da gwamnonin jihohin Arewa da sauran manyan ‘yan Najeriya, sun nuna alhini da ta’aziyya ga tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, kan rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza Jega.
Marigayiyar ta rasu ne kwanan nan, inda aka gudanar da jana’izarta bisa tsarin addinin Musulunci a Abuja.
Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima, ya wakilci shugaban kasa wajen sallar jana’izar, yayin da sauran manyan jami’an gwamnati da iyalai suka halarci taron ta’aziyya.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai mutunci, juriya da kuma matukar goyon baya ga mijinta, musamman a lokacin da yake shugabantar INEC.
Haka kuma, gwamnonin jihohin Arewa karkashin jagorancin gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, sun aika da sakon ta’aziyya ga tsohon shugaban INEC da iyalansa. Sun bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’umma, suna masu addu’a ga Allah da ya bawa iyalanta hakuri da juriyar wannan rashi.
Sauran manyan ‘yan Najeriya da ‘yan siyasa sun nuna alhini, tare da addu’ar Allah ya gafarta mata, ya kuma bawa iyalanta hakurin jure rashin.