Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNDLEA ta kama fasto da matarsa kan zargin safarar miyagun kwayoyi

NDLEA ta kama fasto da matarsa kan zargin safarar miyagun kwayoyi

Wani fasto da matarsa sun fada hannun NDLEA kan zargin safarar kayan maye.

Jami’an Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kama wani fasto da matarsa a Legas bayan gano kilo 11 na tabar wiwi da aka boye a cikin sirrin sassan motarsu.

Wadanda aka kama sun hada da Fasto Afolabi Hodonu mai shekara 45, wanda ake zargin shi ne ke kula da cocin Celestial Church of Christ da ke Agonvi Sea Beach a yankin Sakpo na iyakar Seme a Badagry, da kuma matarsa, Misis Success Hodonu mai shekara 35.

An kama su ne ranar Alhamis, 2 ga watan Afrilu a wurin binciken ababen hawa na Gbaji, kamar yadda Legit Hausa ta gano a shafin hukumar NDLEA.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce binciken da aka yi wa motarsu kirar Honda Pilot ya kai ga gano kayan mayen da aka boye a cikin sassan mota.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments