Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Tinubu ya yi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara kan ta’addanci da matsalar tsaro, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya za ta yi nasara kan ta’addanci da matsalar tsaro, yana mai jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da filin jirgin sama na Gateway International Agro-Cargo da ke Iperu a Jihar Ogun.

Tinubu ya ce tsaro na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, tare da bunkasa tattalin arziki da ayyukan more rayuwa, yana mai cewa zuba jari a fannin tsaro da hadin gwiwar kasa za su taimaka wajen kawar da barazanar tashin hankali.

Ya ce: “Za mu shawo kan tashin hankali da ta’addanci,” yana mai cewa ana hada tsare-tsaren tsaro da manyan shirye-shiryen ci gaba kamar sufuri, noma da makamashi.

Sai dai kalaman nasa sun zo ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da tsananta a wasu sassan kasar.

A Jihar Plateau, bayan ziyarar da ya kai Jos, an sake samun harin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane uku a yankin Nyango Gyel, karamar hukumar Jos South.

Har ila yau, a Jihar Nasarawa, an tabbatar da mutuwar kusan mutane 11 sakamakon rikici tsakanin al’ummomi biyu na Akyawa da Udege Kasa.

Shugaban ya yi alkawarin cewa irin wadannan hare-hare ba za su sake faruwa ba, yayin da ya bukaci jami’an tsaro su dauki matakan gaggawa don kawo karshen wannan matsala.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments