Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMutum 34,000 sun nemi gurbin mutum 1,000 a hukumar ƴan sandan jihar...

Mutum 34,000 sun nemi gurbin mutum 1,000 a hukumar ƴan sandan jihar Benue

Akalla mutane 34,000 ne suka nemi guraben aiki 1,000 na rundunar ‘yan sandan Najeriya a Jihar Benue, kamar yadda jami’an ‘yan sanda a jihar suka bayyana.

Akalla mutane 34,000 ne suka nemi guraben aiki 1,000 na rundunar ‘yan sandan Najeriya a Jihar Benue, kamar yadda jami’an ‘yan sanda a jihar suka bayyana.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Binciken Laifuka da Sirri na Jiha SCIID, Musa Abdulraham, ne ya bayyana hakan jiya yayin wani taro a gidan taron jami’an ‘yan sanda a Makurdi, a cikin shirye-shiryen bikin Makon ‘Yan Sanda na 2026.

Yayin gabatar da takarda mai taken: “Hana Rikicin Zabe da Kwacen Akwatin Zabe,” ya danganta yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasa da yadda suke zama masu sauƙin yaudara daga ‘yan siyasa, wanda ke sa su shiga rikice-rikicen zabe.

Ya ce yawan masu neman aikin ya kai 34,000, wanda hakan ya nuna ƙarancin damar aiki, wanda ke jefa matasa marasa aikin yi cikin hannun ‘yan siyasa da ke amfani da su wajen haddasa rikici a lokacin zabe.

Ya ce: “Misali, a wannan aikin daukar ‘yan sanda da ake yi yanzu, mutane 34,000 ne suka nema a Jihar Benue don guraben aiki 1,000 kacal. Idan aka ba 1,000 aiki, me zai faru da sauran 33,000?”

Ya gargadi cewa rikicin zabe na ci gaba da zama babbar barazana ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya, yana mai cewa irin wannan rikici ya samo asali tun daga zaben yankuna na 1964 wanda ya kara tsananta a shekarar 1965.

“Rikici ba zai inganta zabe ba, sai dai ya lalata shi. Idan ya fara, yana iya fita daga iko ya zama mai matukar illa,” in ji shi.

Musa Abdulraham ya bayyana cewa kwacen akwatin zabe da sauran magudin zabe manyan laifuka ne, yana mai cewa zabukan da suka hada da na shekarar 2023 sun fuskanci nau’o’in rikice-rikice daban-daban.

Ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su magance matsalar rashin aikin yi ta hanyar samar da ayyukan yi, yana mai cewa samar da aikin yi ga matasa zai rage shigarsu cikin rikicin zabe tare da karfafa tsarin zaben kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments