Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiJam'iyyar SDP ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani kan bashin...

Jam’iyyar SDP ta bukaci Bola Ahmed Tinubu ya yi bayani kan bashin Naira triliyan 158 da ya karbo a shekaru 3

Jam’iyyar SDP ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta yi cikakken bayani kan sama da Naira tiriliyan ₦158 na bashin waje da ake zargin an karɓa cikin shekaru uku da suka gabata.

Jam’iyyar SDP ta bukaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta yi cikakken bayani kan sama da Naira tiriliyan ₦158 na bashin waje da ake zargin an karɓa cikin shekaru uku da suka gabata.

Jam’iyyar ta kuma nuna damuwa cewa bashin da Majalisar Tarayya ta amince da shi kwanan nan, za a iya amfani da shi ba ta hanyar daidai ba ko kuma a karkatar da shi domin manufofin siyasa gabanin zaben shekarar 2027.

Shugaban SDP na kasa, Sadiq Abubakar Gombe, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja, inda ya ce babu isasshen shaida da ke nuna cewa an yi amfani da kudaden bashin wajen gina manyan ayyukan raya kasa.

Ya bayyana yawan bashin da aka karɓa a matsayin abin da bai taba faruwa ba, yana mai kira da a samar da cikakken bayani da gaskiya wajen tafiyar da bashin gwamnati da kuma kudaden da aka kwato daga satar dukiya.

Ya tambaya: “Ina kudaden bashin? Wane irin ayyuka aka yi da su, kuma ta yaya suka inganta rayuwar ‘yan Najeriya?”

Jam’iyyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana cikakken bayani kan dukkan kudaden da aka kwato, adadinsu, inda ake adanawa, da yadda ake amfani da su bisa ka’idojin kasa da kasa.

Wannan kira ya biyo bayan amincewar Majalisar Tarayya da karin bashin dala biliyan 6 da shugaban kasa ya nema.

SDP ta gargadi cewa Najeriya ba za ta iya jure sake shiga yanayin karɓar bashi ba tare da bayani da gaskiya ba, tana mai jaddada muhimmancin kula da kudaden gwamnati da tsari mai kyau.

A bangaren tsaro, jam’iyyar ta soki yadda gwamnati ke tafiyar da matsalar tsaro, tana mai cewa dole ne a dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Har ila yau, SDP ta bayyana shirinta na zaben 2027, tana mai cewa tana bude kofa ga duk masu neman mukamai, ciki har da kujerar shugaban kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments