Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiManyan ƴan siyasa da fitattun mutane sun halarci jana'izar mahaifiyar El-Rufa'i.

Manyan ƴan siyasa da fitattun mutane sun halarci jana’izar mahaifiyar El-Rufa’i.

An yi jana’izar Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Malam Nasir El-Rufai, a birnin Abuja ranar Lahadi.

An yi jana’izar Hajiya Umma El-Rufai, mahaifiyar Malam Nasir El-Rufai, a birnin Abuja ranar Lahadi.

An binne ta a makabartar Gudu bayan gudanar da sallar jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci. Rahotanni sun nuna cewa ta rasu ne ranar Juma’a a birnin Cairo, inda take karɓar magani.

Bayan rasuwarta da wasu sa’o’i, hukumar ICPC ta saki El-Rufa’i da ke tsare a hannunta bayan ya shafe sama da wata guda. An kuma hangi fuskokin manyan mutane irinsu Aminu Tambuwal, Rotimi Amaechi, Peter Obi, Sheikh Pantami, da kuma shauran manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane sun halarci jana’izar, ciki har da tsofaffin gwamnoni da na yanzu, da kuma ‘yan adawa.

Haka kuma, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu sun aika saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar.

Sauran manyan mutane kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da shugabannin jam’iyyar APC sun kai ziyara domin jajantawa El-Rufai a gidansa da ke Abuja.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments