Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiAn hangi Nuhu Ribadu a wajen jana'izar mahaifiyar El-rufa'i, duk da rashin...

An hangi Nuhu Ribadu a wajen jana’izar mahaifiyar El-rufa’i, duk da rashin jituwar da ke tsakanin su.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ajiye saɓanin siyasa tsakaninsa da Nasir El-Rufai, inda ya halarci sallar jana’izar mahaifiyarsa a ranar Lahadi.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ajiye saɓanin siyasa tsakaninsa da Nasir El-Rufai, inda ya halarci sallar jana’izar mahaifiyarsa a ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da sallar jana’izar a Masallacin Ƙasa da ke Abuja, sannan aka binne marigayiyar a makabartar Gudu, duk a Abuja.

Daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar akwai shi Ribadun, wanda ya tsaya kusa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

A baya, Ribadu da El-Rufai sun kasance abokan siyasa na kusa kafin rikicin da ya biyo bayan cire El-Rufai daga jerin ministocin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Rikicin ya ƙara tsananta bayan El-Rufai ya zargi Ribadu da hannu a cikin kama shi, inda kuma Ribadu ya musanta zargin tare da kai ƙara ga DSS.

Sai dai bayan rasuwar mahaifiyar El-Rufai, Ribadu ya aika da saƙon ta’aziyya, yana tuna irin rawar da marigayiyar ta taka a rayuwarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments