Sojojin Sashe na 2 na ‘Operation FANSAN YAMMA’ sun hallaka aƙalla ‘yan ta’adda 5 tare da kwato bindigogi AK-47 guda 5 a jihohin Sokoto da Zamfara.
Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soji ta 8, Sashe na 2, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
A cewarsa, sojojin sun kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi domin kare al’umma da kuma kawar da ‘yan ta’adda.