Hukumar kidaya ta Najeriya (NPC) ta ce ta yi rijistar haihuwar yara sama da 36,000 a Kano cikin watanni tara da fara amfani da tsarin rijistar haihuwa ta na’ura.
Daraktan hukumar a jihar, Balarabe Kabir ne ya bayyana hakan a wani taron horaswa da aka gudanar a Kano.
Ya ce an shirya taron ne da hadin gwiwar kungiyar kananan hukumomi ta Najeriya da hukumar da ke rijistar katin dan kasa (NIMC), tare da tallafin gwamnatin Netherlands da kuma UNICEF.
Kabir ya bayyana cewa adadin da aka bayar wani bangare ne kawai na yawan yaran da aka riga aka yi wa rijista, inda ya kara da cewa an kuma tantance yara kusan 27,000 ‘yan kasa da shekaru biyar, da sama da 40,000 da suka haura wannan shekaru, wadanda ba a taba rijistar su ba a baya.