Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati na shirin bai wa matasa horo kan dabarun kwance nakiya don...

Gwamnati na shirin bai wa matasa horo kan dabarun kwance nakiya don yaki da matsalar tsaro – Christopher Musa

Christopher Musa ya sanar da cewa gwamnati na duba yiwuwar horas da matasa kan fannin kwance nakiya don taimakawa yaki da ta’addanci.

Ministan tsaron Najeriya janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana shirin hada tsofaffin sojoji da fararen hula cikin ayyukan kawar da ababen fashewa domin dakile barazanar ababen fashewa IEDs.

Christopher Musa ta bakin babban sakataren ma’aikatar tsaro Richard Pheelangwah ya sanar da hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki kan ayyukan kawar da nakiyoyi da aka gudanar an Abuja.

Ministan ya ce wannan shiri zai taimaka wajen karfafa kokarin da ake yi na rage hadarin nakiyoyi da ake dasa wa musamman a yankunan da ke fama da rikicin ‘yan tada kayar baya.

Ya ce za a kafa kungiyoyin fararen hula masu aikin kwance nakiyoyi, wadanda za su kunshi tsofaffin injiniyoyin soja, kwararrun jami’an tsaro, likitoci da kuma matasa da aka horar.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments