Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan hulɗa da al’umma a shiyyar Arewa maso Yamma, Abdullahi Yakasai, ya bayyana cewa matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Najeriya na shafar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, har ya kai ga yana fama da rashin barci.
Yakasai ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels.
Ya ce duk da cewa an samu sauƙi a wasu sassan ƙasar, sabbin dabarun da masu aikata laifuka ke amfani da su na kawo sabbin ƙalubale.
A cewarsa, shugaban ƙasar na gudanar da tarukan Majalisar Tsaro akai-akai a Fadar Shugaban Ƙasa domin magance matsalar.
Maganganunsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙaruwar hare-haren ‘yan bindiga, satar mutane da sauran ayyukan ta’addanci, musamman a Arewacin Najeriya.
Yakasai ya ce yaƙi da rashin tsaro ya ƙara rikitarwa saboda yadda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da dabarun yaƙin sunƙuru.
Haka kuma, ya yi zargin cewa akwai wasu mutane da ke ƙoƙarin ruruta matsalar tsaro domin bata sunan gwamnati.
Sai dai ya nuna cewa an samu sauƙi a wasu wurare, daga ciki har da wasu sassan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma jihar Zamfara.
A cewarsa, masu aikata laifuka na sauya wuraren aikinsu zuwa wasu jihohi kamar Neja da Kwara.
Yakasai ya bayyana fatan cewa ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi zai haifar da daidaituwar al’amura nan gaba.