Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLokacin cire jar hula bai yi ba, a jira – Gwamnan Kano

Lokacin cire jar hula bai yi ba, a jira – Gwamnan Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce har yanzu lokacin cire jar hula ta Kwankwasiyya bai yi ba, duk da komawarsa jam’iyyar APC.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce har yanzu lokacin cire jar hula ta Kwankwasiyya bai yi ba, duk da komawarsa jam’iyyar APC.

Maganar ta taso ne bayan an gan shi a Yola sanye da kayan da ke ɗauke da tambarin Bola Ahmed Tinubu, inda wasu magoya bayansa suka tambayi ko za su daina sanya har hula.

Sai dai mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce babu umarnin hakan tukuna, yana mai cewa “komai yana da lokacinsa.”

Duk da nesanta kansa daga Rabiu Musa Kwankwaso, gwamnan na ci gaba da amfani da jar hula, wadda wasu ke kallon ta a matsayin alamar siyasa da kuma al’ada a Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments