Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam, International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety), ta bayyana cewa sama da mutane 190,000 ne aka kashe a Najeriya cikin shekaru 17 da suka gabata sakamakon hare-haren ‘yan bindiga, Boko Haram, da makiyaya masu ɗauke da makamai.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan adadi ya shafi lokacin daga watan Yulin 2009 zuwa Maris 2026, inda aka samu asarar rayuka a sassa daban-daban na ƙasar.
Rahoton ya nuna cewa kimanin mutane 128,750 Kiristoci da kuma 61,400 Musulmai ne daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a wannan lokaci.
Haka kuma, ƙungiyar ta bayyana cewa sama da mutane 131,000 an sace su, ciki har da dubban da aka kashe yayin da suke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.
Shugaban ƙungiyar, Emeka Umeagbalasi, ya ce waɗannan alkaluma sun samo asali ne daga bincike da tattara bayanai kan hare-hare, sace-sace da sauran ta’addanci da aka yi a ƙasar tsawon shekaru, kuma rahoton ya nuna cewa hare-haren na ci gaba da ƙaruwa musamman a yankunan Arewa maso Gabas, duk da ƙoƙarin da ake yi na dakile ta’addanci.