Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeSaudiyya ta bai wa jami’an Iran wa’adin awa 24 su fice daga...

Saudiyya ta bai wa jami’an Iran wa’adin awa 24 su fice daga ƙasar

Saudiyya ta bayyana wasu jami’an Iran a matsayin waɗanda ba a maraba da su ba tare da korarsu.

Gwamnatin kasar saudiyya ta umarci jami’an diflomasiyyar Iran da su fice daga kasar nan take.

Sauran da aka kora sun hada da jami’in soja da wasu ma’aikata hudu da su bar kasar cikin awa 24, bayan zargin kai hare-hare akai-akai.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana cewa ta ayyana jami’an a matsayin “wadanda ba a maraba da su,”

Duka wannan mataki na zuwa ne sakamakon hare-haren da take dangantawa da Iran a cikin kasar.

Wannan mataki ya zo ne yayin da rikici tsakanin amurka da isra’ila da Iran ke kara tsananta, inda ake zargin Tehran da kai hare-hare kan kasashen yankin da ke dauke da sansanonin sojojin Amurka.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments