Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhini kan mummunar hatsarin motar da ya afku a Unguwar Okunchi a Ƙaramar Hukumar Adavi.
Ta kuma jaddada cewa za ta tallafa wa iyalan da abin ya shafa.
Gwamna Ahmed Usman Ododo domin jajanta wa al’umma da duba halin da ake ciki.
Hatsarin dai ya faru ne tsakanin tankar diesel da motar simintin BUA, inda gobara mai tsanani ta tashi.
Wutar ta ƙone mutanen da ke cikin tankar gaba ɗaya ba tare da a gane su ba.
Haka kuma gobarar ta lalata wani gida da masallaci, duk da cewa babu asarar rai a waɗannan wuraren.
A wani lamari kuma, wata mota mai ɗauke da fasinja biyu ta gamu da hatsari sakamakon zubewar diesel.
Mijin ya rasu nan take bayan ya kasa sarrafa babur ɗinsa, yayin da matarsa ke jinya a asibiti.
Daga baya kuma direban motar BUA ya rasu bayan an kai shi asibiti, yayin da mataimakinsa ya tsira da rauni.