Rundunar sojin saman Nigeria karkashin Operation
HADIN KAI ta kai hare-hare a dajin Sambisa da ke jihar Borno, inda ta hallaka ‘yan ta’addan Boko Haram da dama.
Majiyoyin tsaro sun ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa ‘yan ta’addan suna taruwa a yankin Parisu cikin dajin.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya yi nasara, inda aka lalata sansanonin ‘yan ta’addan tare da rage karfinsu a yankin.