Akalla mutum 69 sun mutu wasu 89 kuma sun jikkata sakamakon wani harin da aka kai kan wani asibiti a yankin Darfour da ke kudancin Sudan da yammacin jiya Asabar.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban hukumar lafiya ta duniya,Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar kaduwa game da harin da aka kai asibitin koyarwa ta El-Daein da ke Kudancin Sudan inda mutum sama 60 da suka hada da yara kanana 13 suka rasa rayukansu.
Rikicin da ya hada tsoffin aminan juna a Sudan tun daga shekara 2023, ya kazanta bayan da bangarorin biyu suka fara amfani da jirage marasa matuka domin kai hare-hare kan gine-gine jama’a da makarantu da kuma asibitoci.
Yankin El-Daein da ke karkashin ikon mayakan RSF ya na fuskantar hare-hare kai-a-kai daga dakarun gwamnati.