Donald Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social inda yace sun kusa cimma muradunsu don haka suna duba yiwuwar kammala harin da suke yi a kan Iran.
Lamura sun dagule a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare a Iran ranar 28 ga Fabrairu.
Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe aƙalla mutum 1,300, cikinsu har da ƙananan yara mata ‘yan makarantar firamare fiye da 150.