Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeƘasashen Larabawa sun yi Allah-wadai da harin Isra'ila a Syria.

Ƙasashen Larabawa sun yi Allah-wadai da harin Isra’ila a Syria.

Ƙasashen Larabawa sun nuna matuƙar damuwa tare da yin Allah-wadai da hare-haren da Israel ta kai a Syria, suna mai bayyana su a matsayin take ikon ƙasa da kuma cin zarafi.

Ƙasashen Larabawa sun nuna matuƙar damuwa tare da yin Allah-wadai da hare-haren da Israel ta kai a Syria, suna mai bayyana su a matsayin take ikon ƙasa da kuma cin zarafi.

Saudi Arabia, ta bakin ma’aikatar harkokin wajenta, ta ce hare-haren sun shafi sansanonin sojojin Syria, tare da yin kira ga ƙasashen duniya su ɗauki mataki domin dakile irin waɗannan hare-hare. Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta kai farmakin ne a kudancin Syria, tana mai cewa martani ne ga hare-haren da aka kai kan al’ummar Druze a yankin Sweida.

Haka kuma, ƙasashe kamar Egypt, Jordan, Qatar da Kuwait sun haɗa kai wajen Allah-wadai da harin, suna jaddada muhimmancin kare ikon Syria da kuma buƙatar a ɗauki matakin gaggawa daga United Nations Security Council.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta, musamman bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, wanda ya ƙara tayar da hankali a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments