Allah ya yiwa Hajiya Sabuwa ta shirin Dadin Kowa na gidan talabijin na Arewa 24 rasuwa, a daren Alhamis na karshen Ramadana.
An yi jana’izarta a ranar Alhamis da misalin karfe 9.00 na safe a unguwar Dan Maliki Kano.
Masoyanta suna addu’a Allah ya gafarta mata Allah ya bawa iyalanta hakurin rashi.