Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu zai tattauna da Sarki Charles III kan batutuwan tattalin arziki

Tinubu zai tattauna da Sarki Charles III kan batutuwan tattalin arziki

Tinubu zai gana da Sarki Charles III don tattauna harkokin kasuwanci.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na shirin ganawa da Sarkin Birtaniya, King Charles IIl, a yau Laraba, domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasuwanci da kuma gyaran manyan tashoshin ruwa na Nijeriya.

Rahotanni sun nuna cewa Tinubu tare da mai dakinsa, Oluremi Tinubu, sun isa London a ranar Talata domin wannan ziyara ta tarihi wadda ita ce irinta ta farko cikin kusan shekaru 40 tsakanin kasashen biyu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaban zai fara haduwa da Yarima mai jiran gado, Prince William, tare da matarsa Catherine Princess of Wales, kafin daga bisani Sarki Charles ya karbe shi a fadarsa.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments