Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeNajeriya da kasashen Afirka na cikin hadarin yunwa sakamakon yakin Iran da...

Najeriya da kasashen Afirka na cikin hadarin yunwa sakamakon yakin Iran da Isra’ila

Farashin kaya zai tashi a Afirka saboda rikicin Iran da Isra’ila.

Hukumar kula da abinci ta duniya ta yi gargadin halin da za a shiga na yunwa a Najeriya da wasu kasashen Nahiyar Afirka.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kimanin mutane miliyan 10.4 a Yammaci da Tsakiyar Afirka na iya fadawa cikin matsananciyar yunwa idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Rahoton da hukumar ta fitar ya bayyana cewa rikicin da ya hada da Iran da kuma hadin gwiwar isra’ila da Amurka na iya jefa duniya cikin matsalar abinci.

Hakan dai ya biyo bayan barkewar yaki tsakanin Iran da Isra’ila tun a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.

Yakin ya jawo hauhawar farashin man fetur a duniya da kuma wasu kayayyakin masarufi da ake amfani da su.

Shugaba Donald Trump ya ce man fetur zai sauka da zarar an kammala yakin da ake yi ba tare da bata lokaci ba.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments