Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroMutum ɗaya ya mutu a taron sulhun yan daba a Kano

Mutum ɗaya ya mutu a taron sulhun yan daba a Kano

Ƴan sanda sun kama mutum 10 a rikicin daba a Kano

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum guda bayan rikici tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan daba a Kano.

Rahoton ya nuna cewa lamarin ya faru da misalin karfe 10.30 na dare a yankin Ja’en Unguwar Lalle, bayan wani taron sulhu tsakanin bangarorin ya ci tura.

Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa wani mazaunin yankin ya kira yan sa ‘yan, inda sanda suka gaggauta isa wurin, suka shawo kan lamarin.

‘Yan sanda sun kama wasu shugabannin da ake zargi, daga xiki har da Abubakar Abdullahi mai shekaru 22 da Abubakar Bello wanda aka fi sani da Babuji mai shekaru 18.

Mutane uku sun samu munanan raunuka, inda aka kai su asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

Daya daga cikinsu, Aliyu Abdullahi, ya rasu daga baya, yayin da sauran ke ci gaba da karbar magani.

Bincike na ci gabda gudana, inda ‘yan sanda suka sake kama wasu mutum takwas tare da kwato makamai irin su adda, takobi da kuma layu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments