Dakarun sojin Najeriya sun fafata da mayaƙan Boko Haran inda da suka samu nasarar fatattakarsu tare da ƙwato sansaninsu dake ƙarƙashin ƴan ta’addar a garin Ngoshe na jihar Borno.
Rundunar sojin dai ta Najeriya ta yi nasarar a matsayin martani akan mummunan harin da ƴan ƙungiyar ta Boko Haram suka ƙaddamar a garin na Ngoshe ne da zummar tabbatar musu da cewa suma fa sun ɗaura irin tasu ɗamarar.
Dakarun sojin ƙasar sun gudanar da wannan samamen ne na haɗin gwiwa tare da jami’an ƙungiyar tsaron sa kai ta Civilian Joint Task Force (CJTF), da ta ƴan banga da kuma mafarauta.
Idan dai za a iya tunawa ‘yan ta’addan na Boko Haram a makon da ya gabata sun kashe sojoji 14 da fararen hula da dama yayin wani harin da suka ƙaddamar tare da sace mata da yara sama da 100.
A yayin da wata majiyar soji ta bayyana cewa babban kwamandan rundunar sojin Bornon ne, da kansa ya je Pulka inda ya hada dakaru 200 a cikin garin na Ngoshe, inda ya tantance lamarin ya fice tare basu umarnin yin duk abin da ya dace wajen tabbatar da lumana.
Sannan ministan tsaron Najeriya Christopher Musa ya haɗa kan hafsoshin sojin ƙasar an Abuja fadar gwamna domin duba lamuran tsaron dake neman gagarar kundila.