Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiKimanin mutane 69 sun mutu a hare-haren jiragen sama marasa matuƙi a...

Kimanin mutane 69 sun mutu a hare-haren jiragen sama marasa matuƙi a Sudan – Hukumar lafiya

Hukumomin lafiya a Sudan sun tabbatar da mutuwar mutum aƙalla 69, sakamakon hare-haren jiragen sama marasa matuƙi da ya rutsa da su a kudancin ƙasar, ciki kuwa har da ɗalibai mata.

Bayanai sun nuna cewa, wani jirgi mara matuki ya kai hari kan wata motar dakon kaya da ke ɗauke da mutane kusan 90, waɗanda suke kan hanyar zuwa ta’aziyya a garin Al-Foula.

Harin dai ya kashe aƙalla mutane 52, mafi yawancinsu mata ne da ƙananan yara, kuma an kai harin ne a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan Abu Zabad da Al-Foula.

Haka zalika, wani jirgi mara matuki da ake zargin ƴan tawayen RSF ne suka tura, ya harba makamai kan wata makarantar sakandare da cibiyar lafiya a kauyen Shukeiri da ke kusa da Kosti.

Harin ya kashe mutane 17, ciki har da ɗalibai aƙalla mata 9 da malamai 3 sai kuma ma’aikacin lafiya ɗaya.

Ko da yake babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin har yanzu, amma dai ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin sojojin Sudan da ƴan tawayen RSF a yankin Kordofan inda aka kai harin.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar amfani da jirage marasa matuƙa a yaƙin na Sudan, wanda ya jefa rayuwar fararen hula cikin babban haɗari.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments