Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKano: Aminu Ado Bayero ya fara shirin Hawan Sallah, ba a ji...

Kano: Aminu Ado Bayero ya fara shirin Hawan Sallah, ba a ji ta bakin Muhammadu Sanusi II ba

Aminu Ado Bayero ya shirya Hawan Sallah a Kano, babu labari daga Muhammadu Sanusi II.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan sallah yayin da azumin watan Ramadan 2026 ke kokarin karewa.

Alamu dai sun nuna cewa za a sha kallo a jihar Kano kasancewar mai martaba Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan sallah.

Shirye-shiryen hawan sallar da Aminu Ado ya tsara sun dauki hankali ne kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi ma zai iya shirya hawan sallah a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa bayanan da masarautar Kano bangaren Aminu Ado ta fitar ne a wata wasika da fadar shi ta wallafa a shafinta na X.

Fadar Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ‘yan sandan Najeriya a Kano a hukumance kan shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah.

A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga Maris, 2026, wadda aka aike wa kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, majalisar masarautar ta ce za a gudanar da bukukuwan sallah ne daga fadar sarki da ke Nasarawa a Kano.

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kwaru, ya sanya wa hannu, ta ce sarkin tare da mambobin Majalisar Masarautar Kano sun amince da jadawalin ayyukan da za a gudanar.

Bukukuwan da Aminu Ado zai yi A cewar wasikar, bukukuwan Sallah da aka amince da su za su kunshi jerin gwanon Durbar da suka hada da Hawan Sallah, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da Hawan Panisau, tare da sauran wasannin al’adu.

Fadar ta ce cikakkun bayanai na shirin, da suka hada da ranaku, lokuta da wuraren da za a gudanar da jerin gwanon, suna kunshe cikin wani jadawali da aka hada tare da wasikar da aka tura wa hukumomin tsaro.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments