Iran na cigaba da kai hare-hare a kasashen yankin Gulf a matsayin martani kan hare-haren Amurka da Isra’ila.
Oman ta ce an kai hari kan tankokin ajijyar manta da jirage marasa matuƙa.
Tun da farko dai an kai hari kan jiragen dakon man fetur guda uku, ciki har da mai ɗauke da tutar Thailand, wanda ya kama da wuta a lokacin da ya yi yunƙurin wucewa ta mashigar Hormuz.
Tehran ta yi gargaɗin cewa babu jirgin da zai wuce ta mashigar, wadda hanya ce mai muhimmanci wajen kasuwancin man fetur a duniya.