Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeKasashen G7 za su fara sakin man fetur daga rumbunan ajiyarsu

Kasashen G7 za su fara sakin man fetur daga rumbunan ajiyarsu

G7 na shirin bude rumbunan ajiyar man fetur.

Kasashe da dama dai na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G7 sun sanar da cewa za su buɗe wasu daga cikin manyan runbunan ajiyar man fetur da suke da su, a wani yunkuri na kwantar da hankula a kasuwannin makamashi na duniya, yayin da ake ci gaba da yaki da Iran.

Kasashen Japan, Austireliya da Jamus sun ce za su fitar da mai daga rumbunan ajiyar kasashensu.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa hukumar kula da makamashi ta duniya IEA tana neman mambobinta talatin da biyu da su saki gangar mai aƙalla miliyan dari hudu.

Idan hakan ya tabbata, zai zama babban shiga tsakani da hukumar IEA ta yi a kasuwar mai ta duniya.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments