Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hutun idi na shekarar 2026 ga ma’aikatan gwamnati.
Sanarwar dai na zuwa ne yayin da ake shirin kammala azumin watan Ramadan da ake yi a yanzu a fadin duniya.
Sanarwar ta fito ne daga Ma’aikatar Albarkatun Dan Adam da Ci gaban Jama’a wadda ta bayyana ranar fara hutu da tsawonsa bisa dokokin aiki da ake bi, cewar Saudi Gazette.
A cewar ma’aikatar, hutun ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyi masu zaman kansu zai fara bayan kammala aiki ranar Laraba 18 ga Maris.
Za su ci gaba da hutun na kwanaki hudu har zuwa ranar Asabar 21 ga Maris, kafin su koma aiki bisa jadawalin da kamfanoninsu suka tanada.
Game da ma’aikatan gwamnati, galibi ana fitar da jadawalin hutunsu ta takardun hukuma, kuma su ma kan samu kwanaki da dama domin bikin karshen watan Ramadan.
Sanarwar ta taimaka wajen daidaita shirye-shirye tsakanin bangarori daban-daban domin iyalai su tsara tafiya, ziyara da bukukuwan Sallah tun da wuri.