Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijar ta sanar da hutun makarantu a kwanaki 10 na ƙarshe...

Gwamnatin Nijar ta sanar da hutun makarantu a kwanaki 10 na ƙarshe na Ramadan.

Mahukunta a Nijar sun amince da hutun makarantu yayin kwanaki 10 na ƙarshen Ramadan.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sauya kwanakin hutun ƙaramar sallah, inda ta bada umarnin rufe illahirin makarantun Boko tsawon kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadana, a matsayin hutu ga Malamai da kuma ɗalibai a duk faɗin ƙasar.

A baya dai hutun sallah ƙarama a Jamhuriyyar Nijar baya wuce kwana ɗaya zuwa biyu, amma daga yanzu gwamnati ta bada umarnin ƙara adadin, don bai wa Malamai da ɗalibai damar samun lokacin ibada.

Abdou Ɗan Neito, na daga cikin waɗanda suka yi fafutukar ganin an samar da wannan hutu na kwanakin ƙarshen watan Azumi, ga abin da yake cewa dangane da hakan.

⁩

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments