Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHukumar NDLEA ta cafke wani tsohon kansila dauke da kilo 40 na...

Hukumar NDLEA ta cafke wani tsohon kansila dauke da kilo 40 na tabar wiwi a Legas.

Tsadar mai ta ƙaru a Najeriya, inda farashin lita ya zarce N1,000 a wasu wurare.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wani tsohon kansila da ya yi wa’adin mulki biyu a Jihar Legas tare da kama wasu miyagun ƙwayoyi a jihohi daban-daban na ƙasar, a wani ɓangare na ƙara kaimi da suke yi wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a fadin Najeriya.

Wanda ake zargin mai suna Sheleru Sadiq Olalekan, mai shekaru 45, tsohon kansila ne a Ƙaramar Hukumar Ibeju-Lekki ta Jihar Legas kuma a halin yanzu mataimaki ne na musamman ga wani ɗan majalisa.

An kama shi ne a gidansa da ke Ilado a Ibeju-Lekki na Jihar Lagos.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya bayyana cewa jami’an hukumar sun kai samame gidansa ne bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka gano kilogiram 40 na tabar wiwi nau’in skunk, a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan.

A yayin tambayoyi, Olalekan ya bayyana wa hukumar cewa miyagun ƙwayoyin da aka samu nasa ne, haka kuma gidan da aka same su a ciki nasa ne, kamar yadda NDLEA ta bayyana.

Ya kuma tabbatar da cewa a baya ya yi wa’adin mulki biyu inda ya wakilci al’ummar Orimedu a matsayin kansila.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments