Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSaudiyya ta tarwatsa jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka...

Saudiyya ta tarwatsa jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka harbo kasar

Saudiyya ta sanar da cewa ta tarwatsa jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka harba cikin dare.

Ma’aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa dakarunta sun kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da aka kai harba zuwa ƙasar cikin dare.

A cikin wasu saƙonni da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa an gano wani makami mai linzami wanda daga bisani aka kakkabo shi tare da lalata shi a kusa da birnin Al-Kharj, da ke kudu maso gabashin babban birnin ƙasar Riyadh.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa a cikin sa’a ta ƙarshe ma a sake kakkabo wasu jirage marasa matuƙa da dama a kusa da birnin Riyadh.

Jami’an tsaro kasar dai sun ce dakarun ƙasar na aiki don dakile duk wata barazana da ka iya shigowa cikin ƙasar.

Ba a bayar da rahoton jikkata ko asarar rayuka ba zuwa yanzu.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments