Ma’aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa dakarunta sun kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da aka kai harba zuwa ƙasar cikin dare.
A cikin wasu saƙonni da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa an gano wani makami mai linzami wanda daga bisani aka kakkabo shi tare da lalata shi a kusa da birnin Al-Kharj, da ke kudu maso gabashin babban birnin ƙasar Riyadh.
Ma’aikatar ta ƙara da cewa a cikin sa’a ta ƙarshe ma a sake kakkabo wasu jirage marasa matuƙa da dama a kusa da birnin Riyadh.
Jami’an tsaro kasar dai sun ce dakarun ƙasar na aiki don dakile duk wata barazana da ka iya shigowa cikin ƙasar.
Ba a bayar da rahoton jikkata ko asarar rayuka ba zuwa yanzu.