Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƳan majalisar dattawan Amurka sun ƙi goyon bayan kudirin dakatar da yaƙi...

Ƴan majalisar dattawan Amurka sun ƙi goyon bayan kudirin dakatar da yaƙi da Iran.

Kudirin da aka gabatar a Majalisar Dattawan Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin Iran ya fadi.

Majalisar Dattawan Amurka ta yi watsi da ƙudurin da ƴan jam’iyyar Democrats suka gabatar na neman a tilasta wa gwamnatin Shugaba Donald Trump ta dakatar da yaƙin da ake yi da Iran ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.

A kuri’ar 47–53 da aka kada ranar Laraba, Sanatoci sun ƙi amincewa da janye Amurka daga yaƙin.

Sanatocin jam’iyyar Democrats Tim Kaine, Adam Schiff, da Chuck Schumer ne suka gabatar da ƙudirin.

Manufarsa ita ce ta tilasta gwamnatin Amurka ta kawo ƙarshen shiga yaƙin sai dai idan majalisar dokoki ta amince da amfani da ƙarfin soji.

Yawancin sanatocin jam’iyyar Republicans sun ƙi goyon bayan ƙudirin, lamarin da ya dakile yunƙurin farko na majalisar dattawa na takaita hare-haren sama da Pentagon ke kai wa Iran, waɗanda Amurka ke yi tare da Isra’ila.

Sai dai sanatan Republican Rand Paul ya sabawa jam’iyyarsa inda ya kada kuri’ar goyon bayan ƙudirin, yayin da sanatan Democrat John Fettermanya kada kuri’ar adawa da shi.

Kafin a kaɗa kuri’ar, Kaine ya shaida wa manema labarai cewa:

“Bai kamata mu shiga yaƙi ba tare da an tattauna kuma an kaɗa kuri’a a kai ba.”

Shugabannin jam’iyyar Republicans sun kare matakin shugaban ƙasar, suna cewa yana da ikon ci gaba da gudanar da hare-haren sama a kan Iran.

SourceReuters
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments