Farashin ɗanyen mai ya tashi da 10% yayin da kasuwannin makamashi a Asiya suka buɗe a ranar Litinin, ƙari mafi yawa da aka samu tsawon watanni.
Wannan yana nuna haɗarin da ke tattare da jigilar mai ta Mashigin Hormuz da Iran ta ba da sanarwar rufewa.
Tuni dai ƙasashen duniya suka fara shirin tunkarar sakamakon da ke tattare da hakan, la’kari da cewa ta nan ne ake wucewa da aƙalla 20% na makamashin da ake amfani da shi a duniya ciki har da man fetur.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin ruwan Iran na kai hari kan dukkan jiragen ruwan da suka nemi kangarewa umarninsu na ja da baya, harma sun lalata wasu jiragen dakon mai uku.
Kasuwannin hannayen jari da suka buɗe da safiyar nan a Asiya sun fadi warwas.
Akwai fargabar cewa rikicin da ke ci gaba da faruwa zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya.