Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeHarin Iran: Amurka ta umarci ’yan ƙasarta dake Najeriya su zauna cikin...

Harin Iran: Amurka ta umarci ’yan ƙasarta dake Najeriya su zauna cikin shiri

Amurka ta yi kira ga ’yan ƙasarta da ke Najeriya da su nisanci wuraren da ka iya zama haɗari.

Gwamnatin Amurka ta gargaɗi ’yan ƙasarta da ke zaune a Najeriya, biyo bayan ƙara tsanantar rikici tsakanin Amurka da Iran.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, hukumomin Amurka sun shawarci ’yan Amurkawa da ke ƙasashen waje da su kasance masu taka-tsantsan, sakamakon ci gaba da ayyukan soji da suka shafi Iran.

Sanarwar ta ce: “Bayan kaddamar da ayyukan sojin Amurka a Iran, ya kamata ’yan Amurka a sassa daban-daban na duniya, musamman a Gabas ta Tsakiya, su bi umarnin tsaro na baya-bayan nan da ofishin jakadanci ko karamin ofishin jakadancin Amurka mafi kusa ya fitar.”

Gargaɗin ya kuma nuna cewa ’yan Amurka na iya fuskantar tsaiko ko cikas wajen tafiye-tafiye, sakamakon rufe sararin samaniya lokaci zuwa lokaci, abin da ke da nasaba da rikicin da ke kara ta’azzara.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments