Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeA shirye muke mu gwabza dogon yaƙi da Amurka - Iran

A shirye muke mu gwabza dogon yaƙi da Amurka – Iran

Iran ta bayyana cewa ta shirye take tsaf domin yin dogon yaki da Amurka

Sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani ya ce ƙasar a shirye take don gwabza yaƙi mai tsawo saɓanin Amurka.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shifinsa na X ya ce fiye da shekara 300 Iran ba ta taɓa tsokano faɗa ba, kuma dakarun sojinmu ba su taɓa shiga wani yaƙi ba sai na kare kai.

”Don haka duk abin da zai faru, za mu kare kanmu, kuma za mu yi amfani da kafuwar daularmu na tsawon shekara 6,000 don tabbatar da ganin maƙiya ba su samu nasara a kanmu ba”, kamar yadda ya wallafa.

Tun da farko dai sakataren tsaron Amurka ya bayyana a wani taron manema labarai cewa harin da Amurka ta ƙaddamar an Iran har abada ba ne.

”Maƙasudinsa shi ne lalata makaman linzamin ƙasar da rundunar sojin ruwanta da sauran kayayyakin sojin ƙasar”, in ji shi.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments