Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ta ya Aisha Buhari murnar cika shekaru 55.

Tinubu ya ta ya Aisha Buhari murnar cika shekaru 55.

Bola Tunibu ya mika wa Aisha Buhari sakon ta ya murnar cika shekaru 55

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ta ya Uwargidan tsohon Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, murnar cika shekaru 55 a duniya, yana mai bayyana ta a matsayin mace mai jarumtaka da tsayawa kan gaskiya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana Hajiya Aisha Buhari a matsayin mace mai ƙarfin hali wadda ba ta jin tsoron tsayawa ita kaɗai kan abubuwan da ta yi imani da su da kuma manufofinta.

Tinubu ya kuma ya ba da ayyukan jin ƙai da take yi ta hanyar gidauniyarta, Aisha Buhari Foundation, wadda ke kare haƙƙin mata da yara tare da tallafa wa iyalai masu buƙata a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Shugaban ya gode mata bisa gudummawar da ta bayar ga ƙasa tare da yabon juriyarta da ladabinta.

SourcePremier
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments