Hukumar ‘yan sanda ta cafke wani mai gadi mai suna Ismail Obafunsho bisa zargin fasa wani shago tare da kwashe kayan kimanin Naira miliyan biyu da dubu ɗari biyu a garin Ota na Jihar Ogun.
Hukumar ta kuma gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata Kotun Majistare da ke Ota inda yake fuskantar tuhume-tuhume guda uku da suka haɗar da haɗa baki domin aikata laifi, fasa shago, da sata.
Sai dai wannan mai gadi da ke zargi ya ya musanta duk tuhume-tuhumen da ake masa inda kotu ke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.