Gwamnatin Jihar Kano ta gargadi jama’a da ƙungiyoyi kan liƙa fastoci, alluna talla da tutoci a tituna da sauran wuraren gwamnati a cikin birnin Kano.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta fitar, ta bayyana damuwarta kan yadda ake ɓata ababen more rayuwa na jama’a, musamman shataletalen hanyoyi, tsakiyar tituna, gefen hanyoyi, gadar sama da sauran wuraren da aka kawata a cikin birnin.
Ma’aikatar ta ce wannan dabi’a na rage ƙimar ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawata birni da farfaɗo da muhalli, tare da haddasa gurɓacewar yanayi, lalacewar kayayyakin more rayuwa da kuma rage ganin hanya a manyan tituna.
Sanarwar ta ƙara da cewa a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ana gudanar da gyare-gyare da kawata hanyoyi a sassan birnin domin daidaita su da ƙa’idojin gine-ginen birane masu jure sauyin yanayi kamar yadda ake yi a duniya.
Saboda haka, ma’aikatar ta sanar da ‘yan siyasa, kamfanoni, masu shirya taruka, ƙungiyoyin addini, hukumomin talla da sauran jama’a cewa haramun ne amfani da hanyoyi da tsakiyar tituna wajen liƙa fastoci ko duk wani abu na talla ba tare da izini ba.
An kuma umarci sassan da ke kula da doka su ƙara sa ido domin tabbatar da bin ƙa’idojin tsaftar muhalli da kula da birane.
Sanarwar ta ce duk wanda aka kama da karya dokar zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, kuma zai ki ɗauki nauyin gyaran duk abin da ya lalace.