Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya taya waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers murna

Tinubu ya taya waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers murna

Shugaba Tinubu ya taya wadanda suka lashe zabe murnar samun nasara

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya murna da waɗanda suka yi nasara a zaɓukan Abuja da jihohin Kano da Rivers.

A ranar Asabar ne dai INEC ta jagoranci gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomin Abuja, babban birnin ƙasar da na cike gurbi a jihohin Kano da Rivers.

Shugaba Tinubu ya buƙaci waɗanda suka yi nasara a zaɓukan da su nuna kishin ƙasa da sadaukarwa, sannna su auki nauyin da al’umma suka ɗora musu da muhimmanci ta hanyar riƙon amana da aiki da gaskiya.

Jam’iyyar APC ce ta lashe ƙananan hukumomi biyar cikin shida na Abuja, yayin da PDP ta samu ɗaya.
Shugaban Najeriyar ya yaba wa ministan Abuja, Nyesom Wike saboda muhimman nasarorin da ya cimma waɗanda Tinubun ya ce sun taimaka wa APC samun nasara a zaɓukan.

A zaɓukan cike gurbin Yan majalissar jihohin Kano da Rivers ma jam’iyyar APCn ce ta yi nasara a duka kujerun.

Haka kuma Shugaba Tinubu ya yaba wa hukumar za ben kasar INEC, da jami’an tsaro da ma waɗanda suka fita domin kaɗa ƙuri’ar, wadda ya ce an yi cikin kwanciyar hankali da lumana.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments