Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi...

NDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi don ɓoye ƙwayoyi

Hukumar NDLEA ta Najeriya ta kama Rabi Muhammad mai zaune a Kano bayan ta kifa ƙwarya a cikinta domin yin cikin bogi, inda ta naɗe cikin da ƙyalle mai ruwan hoda sannan ta ɓoye kafso 3,200 na ƙwayar Tramadol, a yunƙurinta na tsallakawa cikin Cotonou.

NDLEA ta kama matar da ta kifa ƙwarya a matsayin cikin bogi don ɓoye ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ɗin ta ce matar ta ɓoye kafso 3,200 na ƙwayar Tramadol a cikin ƙwaryar wadda take da niyyar kaiwa Cotonou domin ta sayar.

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) sun daƙile wani yunƙuri na ban mamaki da masu fataucin miyagun ƙwayoyi biyu suka yi na safarar hodar Iblis da miyagun ƙwayoyi da suka ɓoye a cikinsu, da kuma wata mata da ta yi cikin bogi inda ta ɓoye ƙwayoyin a ciki.

An kama ɗaya daga ciki a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, ɗaya kuma a kan iyakar Seme da ke Legas domin tsallakawa zuwa Turai da wasu wuraren.

A ranar Litinin 16 ga Fabrairu, jami’an NDLEA sun kama wata mata ‘yar kasuwa da ke zaune a Kano mai suna Rabi Muhammad mai shekara 35 a kan iyakar Seme a yunƙurinta na shiga Cotonou.

Bayan jami’an na NDLEA sun gama caje ta, sai suka gano ta kifa ƙwarya a cikinta domin yin cikin bogi, inda ta naɗe cikin da ƙyalle mai ruwan hoda kamar yadda wani bidiyo da hukumar ta NDLEA ta wallafa ya nuna.

Hukumar NDLEA ɗin ta ce matar ta ɓoye kafso 3,200 na ƙwayar Tramadol a cikin ƙwaryar wadda take da niyyar kaiwa Cotonou domin ta sayar.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments