Shugaban Amurka, Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa wannan tattaunawa ta na da matuƙar muhimmanci, kuma yana sa ran za ta haifar da ɗa mai ido, inda ya ce baya tunanin Tehran ta shirya tunkarar abin da zai biyo baya idan har ba su cimma yarjejeniya ba.
A yayin da wasu ke fargaba kan sakamakon tattaunawar ta yau, mataimakin ministan harkokin Iran kan fannin tattalin arziƙi Hamid Qanbari ya sanar da shirinsu na gabatar wa Amurka tayin ƙulla cinikayya da zuba jari kan samar da makamashi, da haƙar ma’adanai da cinikin jiragen sama a ƙarƙashin yarjejeniyar Nukiliyar da suke ƙoƙarin ƙullawa.
Akwai dai wasu bayanai da ke cewa Amurka da Isra’ila sun ɗaura aniyar ƙara matsin lamba ga tattalin arziƙin Iran, ta hanyar taƙaita wa ko ma hana Iran ɗin saida wa China man fetur, wadda ke sayen kusan kaso 80 cikin 100 na man da ƙasarr ta Iran ke fitar wa.
Daga nan ne, aka shiga takun-saka da yaƙin cacar baka tsakanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani su amince da shiga tattaunawa a Oman, inda a yau Talata za a shiga zagaye na biyu don ƙulla yarjejeniya.