Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin Najeriya sun dakile hare-haren ISWAP da Boko Haram a Jihar Borno

Sojojin Najeriya sun dakile hare-haren ISWAP da Boko Haram a Jihar Borno

Sojoji sun yi nasarar dakile wani harin yan boko haram

Dakarun rundunar haɗin gwiwa na Operation haɗin kai, sun dakile wasu hare-hare da ake zargin mayakan Boko Haram da na ISWAP da shirya kaiwa garuruwan Pulka da Mandaragirau dake Jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba, ya fitar ranar Litinin, ya ce hare-haren sun faru ne a daren Asabar, lokacin da ‘yan ta’addar suka yi yunkurin kwace sansanonin sojoji a wurare biyu.

Sojojin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan, da suka fito daga wani yanki na dajin Sambisa, sun kai mummunan farmaki kan dakarun Sashe na 1 a Pulka. Sai dai sojojin sun yi artabu mai tsanani da su, inda suka dakile harin tare da tilasta musu ja da baya.

Sanarwar ta ce, duk da cewa an samu keta wani sashe na katangar tsaro na ɗan lokaci wanda ya janyo lalacewar wasu kayan aiki na yaki da gidajen kwana kafin isowar ƙarin dakarun Brigediya ta 26 cikin gaggawa, wanda hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa zuwa dajin Sambisa.

SourceIconic Fm
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments