Majalisar koli ta addinin musulunci a Najeriya ta bukaci Musulmi a fadin kasar nan da su fara duban jinjirin watan Ramadan 1447 A.H. bayan faduwar ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga Sha’aban 1447 bayan hijira.
A sanarwar da babban sakataren majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede ya sanya wa hannu, ta ce kwamitin duban wata na kasa tare da hadin gwiwar hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya, za su kula da aikin tabbatar da ganin watan.
Majalisar ta bayyana cewa idan an ga jinjirin watan a daren Talata, Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar, Muhammad Sa’ad Abubakar, zai sanar da Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026 a matsayin ranar farko ta azumin Ramadan. Idan kuwa ba a ga watan ba, Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 za ta zama ranar farko ta azumin.
Baya ga batun Ramadan, NSCIA ta nuna damuwa kan abin da ta kira karuwar nuna wariya ga Musulmi da yada labaran da ba su dace ba a kafafen yada labarai. Ta ce Musulmi na fuskantar hare-hare daga masu tada kayar baya da ‘yan bindiga, tare da zargin ana musu kallon da bai dace ba a wasu rahotanni.
Har ila yau, majalisar ta bayyana cewa ta samu koke-koke kan jadawalin zabe da INEC ta fitar, inda aka tsara gudanar da zaben shugaban kasa a lokacin Ramadan, da kuma yiwuwar zaben gwamna a ranar Sallah. Ta ce tana sa ran a sake duba jadawalin.