Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Goshwe Yilwatda da sauran jagororin jam’iyyar na jihar Kano a gidan gwamnati a daren Lahadi.
Wannan na cikin shirye-shiryen babban taron karɓar gwamnan a hukumance cikin jam’iyyar ta hannun Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima a yau Litinin.
Sauran jagororin APCn sun haɗa da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Barau Jibrin, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, ƙaramin ministan gidaje, Yusuf Ata, Kabiru Alhassan Rurum, Tijjani Abdulkadir Jobe, Nasiru Yusuf Gawuna, Murtala Sule Garo, Abdullahi Tijjani Gwarzo, AA Zaura da sauran su.