A yau ne dai ake sa ran tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai zai amsa gayyatar EFCC inda zai bayyana a ofishinta da misalin karfe 10 na safe, kamar yadda ya shaida wa BBC a wata hira da tayi da shi.
El-Rufai ya bayyana a ranar Juma’ar da ta gabata cewa hukumar ta aike masa da takardar gayyata zuwa ofishinta, kuma ya amince zai je ofisihin a yau Litinin.
Lamarin na zuwa ne bayan rahotannin da suka ce jami’an tsaro sun ƙwace fasfonsa a Filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe jim kaɗan bayan dawowarsa daga Masar.
Da yake ƙarin bayani kan wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, El-Rufai ya ce ba shi ne ya yi musayar kalamai da jami’an DSS ba, sai dai su ne suka tare shi a filin jirgi suka buƙaci ya bi su ofishinsu.
Ya ƙara da cewa babu wata doka a Najeriya ko ƙundin tsarin mulki da ta ba da damar a tare mutum ba tare da takardar gayyata ko sammaci ba.
Tsohon gwamnan, wanda ke cikin jagororin adawa a jam’iyyar ADC da ke shirin ƙalubalantar shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, ya zargi gwamnati da matsin lamba kan ‘yan adawa ta hanyar kama su da sunan binciken rashawa.
Ya kuma ce an riga an kama kusan mutane huɗu da suka yi aiki tare da su a Jihar Kaduna, yana mai cewa yana ganin lokaci ne kawai kafin a gayyace shi, abin da yanzu ya tabbata yayin da ake sa ran zai bayyana a gaban EFCC a yau domin amsa tambayoyi.