Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojojin sun ceto mutane takwas da aka sace yayin kai Amarya a...

Sojojin sun ceto mutane takwas da aka sace yayin kai Amarya a Shanono

Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto mutane takwas da aka sace a Shanono

Dakarun rundunar Birgediya 3 ta Sojojin Najeriya sun ceto mutane takwas cikin goma da wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka sace a wurin bikin aure a Dabawa, ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano.

Wata majiya daga shalkwata soji ta shaida cewa maharan, waɗanda aka ce sun sanya kayan sojoji, sun kai hari tare da yin awon gaba da mutanen.

Dakarun da ke sintiri a bakin Kogin Yankwada sun hanzarta kai ɗauki bayan samun rahoton lamarin, inda suka yi artabu da maharan a ƙauyen Garu da ke maƙwabciyar Jihar Katsina.

An ce sojojin sun bi sawun maharan har zuwa kan titin Katsina–Gidan Mutum daya kafin aka rasa inda sukaa yi.

A yayin farmakin, an samu nasarar ceto ’yan mata takwas daga cikin waɗanda aka sace, kuma tuni aka miƙa su ga iyalansu.

Majiyar ta ƙara da cewa ana ci gaba da sintiri a yankin domin gano sauran mutane biyun da har yanzu ba a ceto su ba, tare da ɗaukar matakan hana sake faruwar irin wannan hari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments