Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa birnin Addis Ababa a ranar Alhamis domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar Shugabannin Kasashen Afirka (AU) karo na 39.
Shettima ya jagoranci wata tawaga daga Najeriya da ta sauka a filin jirgin sama na Bole kafin manyan abubuwan da za a gudanar a taron ranar 14 da 15 ga Fabrairu, 2026, kamar yadda Ministan Harkokin Waje, Jakada Yusuf Tuggar, ya sanar.
An tarbi Shettima da wasu manyan baƙi daga Najeriya da Ethiopia, ciki har da Ministan Kirkire-kirkire da Fasaha na Ethiopia, Dr. Belete Mola da Ministan Harkokin Wajen Ethiopia, Berhanu Tsegaye, da Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Harkokin Waje, Dunoma Ahmed.
Ministan Harkokin Waje ya bayyana wa Mataimakin Shugaban Kasa yadda taron zai gudana da kuma manufofin Najeriya a taron.
Wannan shekarar, taron AU zai mayar da hankali kan samar da ruwa mai dorewa da ingantaccen tsaftar muhalli don cimma manufofin da aka tsara na 2063.
Wannan dai yana da muhimmanci ga lafiya, noma, da ci gaban kasashen Afirka gaba ɗaya.